(ABNA24.com) An fara gudanar da zaben raba gardama na sauye-sauyen da aka gudanar a kundin tsarin mulkin kasar Rasha a ranar Alhamis 25 ga watan Yuni. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa za’a dauki kwanaki 7 cur ana kada kuri’a saboda matakan hana yaduwar cutar wanda gwamnatin kasar ta dauka.
Labarin ya kara da cewa sauye-sauyen da aka aiwatar a cikin kundin tsarin mulkin kasar dai sun hada da bawa shugaban kasa mai ci Vladimir Putin damar sake tsayawa takarar shugabancin kasar har sau biyu, wato tsawon shekaru shida-shida kowannensu, bayan ya kammala wa’adin da yake kai , wanda zai kare a shekara ta 2024.
Idan har haka ya tabbata, shugaba Putin zai ci gaba da shugabancin kasar har zuwa shekara ta 2036 kenan. Kafin zaben dai majalisun dokokin kasar ta Rasha biyu sun amince da sauye-sauyen sannan shi shugaban kasar, tuni ya sanya mata hannu.
Shugaban kasar ta Rasha ya bukaci mutane su fito don ka’da kuri’unsu don hakan zai taimaka wajen karfafa al-amuran kasar.
/129